Allah Ke Kaunar Kwankwaso, Amma Akwai Matsala A Fitar Da Ake A Kwankwasiyya

 Kwankwaso, Amma Akwai Matsala A Fitar 

Da Ake A Kwankwasiyya.



ALLAH KE KAUNAR KWANKWASO, AMMA AKWAI MATSALA A FITAR DA AKE A KWANKWASIYYA.
Rubutawa: Abubakar Lecturer
Bana Son Ambatar Kalmar ‘Matsala’ Saboda Ba Abar So Bace.
Ina Son Inja Hankalin Dukkan Yan Uwana Matasa Yan Social Media Akan Dan Allah Su Daina Damuwa Akan Fitar Wasu Daga Kwankwasiyya, Wadanda Wallahi Kwankwaso Ne Yake Binsu Bashi Ba Suna Suke Bin Kwankwaso Bashi Ba, A Tsaya Lissafa Taimakon Da Dakta Rabiu Musa Kwankwaso Yayi Musu Bata Lokaci Ne Domin Kowa Ya Sani.
Karku Manta Gwamnati Muke Shirin Karba 2019 Da Yardar Allah, Daga Hannun Ganduje Zuwa Hannun Abba K. Yusuf, Kuma Ba Abune Mai Wahala Ba Domin Al’ummar Jihar Kano Basa Tare Da Ganduje, Sunsan Kwankwaso Mai Kaunarsu Ne Kuma Bazai Cucesu Ba.
Matsalar Itace Dukda Lusarancin Gwamnatin Ganduje, Amma Yana Dakyau Mu Kara Kaimi Wajen Tallata Yan Takararmu Na PDP, Idan Muka Zauna Bamu Da Aiki Sai Idan Wane Ya Fita Muyi Ta Posting Iri Iri, To Tabbas Ana Kokarin Dauke Hankalinmu Akan Abinda Mukeyine Domin Sunsan Cewa Kwalliya Tana Biyan Kudin Sabulu, Dan Haka Babu Wanda Aka Daure Duk Wanda Zai Fita Ya Fita, Nasara Daga Allah Take Shi Kadai, Wallahi Idan Duk Jagororin Kwankwasiyya Zasu Fita Bani Da Damuwa Domin Basu Isa Su Hana Engr. Abba Kabir Yusif Zama Gwamnan Jihar Kano Ba. Ubangiji Allah Ya Bamu Nasara. Ameen.
by kadunaweb.com
20/12/2018.



No comments

Theme images by fpm. Powered by Blogger.