Jigan Jigan Kwankwasiyya 5 Da Sanata Zarewa Sun Fice Saga Kwankwasiyya Zuwa APC Gandujiyya

Jigan Jigan Kwankwasiyya 5 Da Sanata Zarewa Sun Fice Saga Kwankwasiyya Zuwa APC Gandujiyya


Jigan jigan Kwankwasiyya 5 da Sanata Zarewa sun fice daga kwankwasiyya zuwa APC Gandujiyy.
Rahotanni da muke samu da Dumi Duminsa daga Daily Nigeria na nuni da cewa a daren jiya laraba wakilan shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamna Ganduje sun kammala wata ganawar sirri da Sanata Isah Yahaya Zarewa tare wasu jiga jigai kuma fulogan Sanata Kwankwaso inda suka cimma matsaya ta komawa jamiyyar APC Mai mulki bayan sun dangwarar da shahadarsu ta kungiyar kwankwasiyya
Wadanda suka sauya shekar sune
1.Tsohon shugaban hukumar kula da tasoshin jiragen ruwa na kasa Arch. Aminu Ibrahim Dabo
2. Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano farfesa Hafizu Abubakar
3. Tsohon ma’ajin jamiyyar APC na kasa Alh Bala Gwagwarwa
4.Engineer Muazu Magaji
5. Alh Babangida Sulengaro
6. Sanata Isa Yahaya Zarewa
Majiyarmu ta bayyana mana cewar idan ka cire Sanata Zarewa dukkaninin masu canza shekar manyan fulogai ne a kungiyar kwankwasiyya kuma makusanta ne ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
#Najeriyarmu A Yau by kadunaweb.com

No comments

Theme images by fpm. Powered by Blogger.