An Dakatar da Wadansu Sarakunan
An Dakatar da Wadansu Sarakunan Zamfara Kan Zargin Su Da Hanu A Sace Mutani Da Akeyi Aka Jihar
Gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta ce ta dakatar da wasu sarakuna daga mukamansu bisa zarginsu da alaka da ‘yan fashin shanu da masu garkuwa da mutane.
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautun jihar, Alhaji Bello Dankande, ya shaida wa mA’ajiyarmu cewa an dakatar da hakimai uku sannan na hudu ya gudu.
“Duk wani basaraken da ka ga mun dakatar, mun samu labari yana mu’amala da wadannan ‘yan ta’adda. Misali, akwai wani uban kasa da aka kawo mana korafi a kansa cewa, na daya, ya tura galadimansa ya karbi belin barayi daga hannun ‘yan sanda.
“Haka kuma ya karbi kudi daga hannun wani dan ta’adda. Mutanen garin sun zo sun ce ya karbi N50,000,” in ji kwamishinan.
Ya kara da cewa za a gudanar da bincike kan hakiman sannan a tube rawunan da ke kansu “kafin a gabatar da su a gaban shari’a.”
Matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa da kuma ta barayin shanu ta yi kamari a jihar Zamfara, inda a wasu lokutan barayin suke kashe mutanen da suka sace.
Ko da a makon jiya sai da wasu rahotanni suka ce an bayar da kudin fansa kafin a sako wasu tagwaye ‘yan mata da aka sace a jihar.
Gwamnatin jihar ta sha cewa tana daukar mataki domin shawo kan matsalar, ko da yake ana zarginta da hannu a batun amma ta musanta zargin.
Sharhi kan tarihin rikice-rikice a Zamfara – Daga Kadariyya Ahmed
Gwamnatocin da suka mulki kasar a jejjere sun ta yin buris wajen kawo maslaha ta dindindin kan matsolin da ke addabar jihar Zamfara.
Gwamnatocin da suka mulki kasar a jejjere sun ta yin buris wajen kawo maslaha ta dindindin kan matsolin da ke addabar jihar Zamfara.
A yayin da matsalar barayin shanu ta zama bala’i ga jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari ya samar da kungiyar ‘yan kato da gora don yakar maharan a shekarar 2013.
Sai dai ba a dauki dogon lokaci ba mazauna yankin suka fara korafi kan ‘yan kato da gorar, wadanda a yanzu su ma suke gallabar mutanen da ya kamata su kare da sace-sace.
Hakan ta sa kauyukan da ke fama da matsalar barayin shanu da ‘yan kato da gora suka fara kokarin ganin sunkare kansu da duk abun da ya kamata.
Daga haka sai rikicin ya kara ruruwa ta hanyar kai hare-hare da daukar fansa. A haka sai a ka kasa cimma kokarin shirin yin afuwa da aka so gabatarwa.
A yanzu dai muna ganin yadda rikici ke kara bazuwa da karuwa kuma ga alama ba a san hanyoyin da za a bi a shawo kansa ba.
Abun da yake a bayyane kawai shi ne yadda dumbin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ke ci gaba da mutuwa.
No comments