Rububin karanta littattafan soyayya a Nigeria

Rububin karanta littattafan soyayya a Nigeria



Matan aure da 'yan mata a arewacin Nigeria, na matukar son karanta littattafan adabi da ake rubuta su da Hausa wadanda aka fi sani da ''Littattafan Soyayya ko Kasuwar adabin Kano.''
Yawanci a kan rubuta akan rubuta wadannan littattafai ne kan batun zamantakewar al'ummar Hausawa, da soyayya da al'ada da sauransu.
Kasuwar adabin Kano na bunƙasa sosai ganin yadda mata ke ƙaunar karanta littatafan, waɗanda yawanci mata ke rubuta su.
Hadiza Ibrahim Kabuga, wata matashiya ce mai shekara 23, wadda take ƙaunar karanta irin waɗannan littatafai, ta ce, ''Ina karantasu ne don na koyi yadda zan dinga warware matsaloli masu sarƙaƙiya tsakanin budurwa da mai neman aurenta da kuma na rayuwar zaman aure.''
Ɗaya daga cikin irin waɗannan littattafai ''A Daren Farko,'' wanda ya taɓo batun yadda al'amura ke gudana a daren farko na amarci, ya samu karɓuwa sosai a wajen matan aure da 'yan mata.
Littattafan sun zama wasu hanyoyin tattauna batutuwan da ba a cika fayyace su ba a tsakanin mata a arewacin Najeriya.
A wasu lokutan a kan nuna banbanci tsakanin maza da mata, inda wasu iyayen suka yi amannar cewa ba lallai ne yara mata su je makaranta ba, aure shi ne ya fi muhimmanci a gare su.
Matsalar aure fiye da ɗaya'
Fauziyyah D Suleiman wata marubuciya ce wadda ta rubuta littatafan soyayya 32, kuma tana samun kuɗi sosai a wannan sana'a, ta ce, ''Ni a rubuce-rubucena na fi mayar da hankali kan zaman aure da matsalolin kishiyoyi da kuma muhimmancin ilimi.''
Tuni aka samu nasarar mayar da uku daga cikin littattafan nata zuwa fina-finan Hausa.
Akwai wani littafi da Fauziyya ta ubuta mai suna Rumaysah, wanda labari ne na wata mata mai tsananin kishi da ta yi ruwa ta yi tsanaki don ganin ta hana mijinta aure, har ma ta yi yunƙurin hallaka shi.
An rubuta littattafai kan irin wannan labari da ke taɓo rayuwar gidajen aure masu mata fiye da ɗaya da yawa.
Wasu kuwa sun yi duba ne kan yadda ake aurar da yara mata masu ƙananan shekaru, inda yaran kan bijire su nuna sun fi son yin karatu tukunna.
Wani mai sharhi a kan adabi Murtala Abdullahi, ya ce ''Waɗannan littattafai suna kawo sauyi sosai kan yadda ake yi wa mata a ƙasar Hausa.''
Ya ƙara da cewa, ''Littattafan Hausa na soyayya su kan nuna daraja da muhimmancin mata a matsayinsu na uwaye kuma iyayen gida, sannan kuma masu fafutuka kuma ƙwararru.''
'Farashin littattafan'

A kan sayar da kowane littafi ɗaya a kan naira 300, kimanin dala 1.50, kuma ana sayar da su a rumfuna cikin kasuwanni.
Ali Mai Litattafai, wani mai sayar da irin waɗannan littattafai ne a birnin Kano, ya ce, ''A Kowanne mako a kan samu sabbin littattafai a kalla biyar a kasuwa, wasu a kan sayar da dubbansu.''
Ya ƙara da cewa, ''A can baya mutane ba su fahimci saƙon da littattafan ke ɗauke da su ba, don haka suna yawan kushe su, amma yanzu jama'a sun fahimci cewa waɗanann littattafai suna koyar da kyawawan ɗAbi'u.''
A ɗaya daga cikin shagunan sayar da littattafan na ga wani yaro da ya zo sayo wa mahaifiyarsa, saboda wasu matan ba sa samun damar fita sakamakon kulle da ake musu, dole sai dai su aiko.
Yawancin masu sayen littattafan dai matan aure ne, da yawansu kan sayi littatafan da yawa domin su dinga bayarwa haya a unguwanninsu kan farashi ƙalilan.
A kan bayar da hayar littafi ɗaya kan naira hamsin.
'Karanta littatafai a rediyo'
Ana kuma karanta waɗannan littattafai a rediyo.
Gidan rediyon Express FM na Kano sun ware lokacin karanta waɗannan littattafai a kwanaki biyar cikin mako, daga Litinin zuwa Juma'a da misalin karfe tara na safe. Kuma mutane suna raja'a wajen sauraron shirin har tsawon minti talatin.
Haka kuma mutanen ƙauyuka ma kan saurara.
Wakilin BBC Naziru Mika'ilu ya ce, ''A lokacin da yake koyarwa a makaranta na sha kama 'yan mata suna ɓaye littafi a hijabinsu suna karantawa lokacin darasi.''
Malaman addinin da dama sun sha yin suka kan rubuta irin waɗannan littattafai, a cewarsu suna lalata tarbiyar mutane.
A shekarar 2007 ne gwamnan Kano na wancan lokacin ya bayar da umarnin ƙona dubban littattafan soyayya a makarantu.
Daga nan sai aka kafa wata hukuma ta tace littattafan da duk aka rubuta kafin a wallafa su, domin a cire duk wani abu da bai dace ba.
Amma daga baya wannan mataki ya yi sako-sako bayan da marubutan suka yi nasarar lashe wata shari'a a kotu da aka ba su damar 'yancin faɗin albarkacin baki.
'Jin ta bakin makaranta'
Yawanci marubutan kan rubuta lambar wayarsu a bangon littafin, domin su samu damar jin ta bakin makarantansu kan yadda suka karɓi saƙon nasu.
A wasu lokutan kuwa wasunsu na samun saƙonnin barazana, inda ake yi musu umarnin daina rubutun.
Maryam Salisu Maidala, wata Malamar makaranta ce da ta rubuta littatafai biyu da suka samu karɓuwa sosai, ta ce ba a taɓa kiranta a waya an yi mata barazana ba, sai dai ma saƙonnin da take samu na yabo da jinjina musamman kan wani littafinta mai suna ''Kainuwa.''
Ta ce, ''Wani lokacin ma makaranta kan kirani su tambayeni ko labarin da na rubuta da gaske ya faru
'Ƙalubale daga kafafen sadarwar zamani'

No comments

Theme images by fpm. Powered by Blogger.