Na fi duk wani kocin firimiya — Mourinho

Na fi duk wani kocin firimiya — Mourinho




Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce ya fi duka masu horas da kungiyoyin gasar firimiya a halin yanzu, "don sau uku ina lashe kofunan gasar," a cewarsa.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan rashin nasarar da kungiyarsa ta yi a gida a hannun Tottenham a ranar Litinin.

A taron da ya yi da manema labarai bayan wasan, kocin Manchester United, Jose Mourinho, ya fusata.

Da yake magana kan shan kayen da Man U ta yi a Old Trafford, Mourinho ya ce idan mutane sun san ma'anar kwallaye ukun da aka sha Man United, to za su san cewa shi ya fi sauran masu kula da kungiyoyin gasar Firimiya.

Mourinho ya ce, hakan ya faru ne domin shi ya ci gasar Firimiya sau uku yayin da duka sauran takwarorinsa na gasar firimiya a yanzu sun ci gasar ne sau biyu kacal jumulla.

Sai dai dan wasan gaban Tottenham, Harry Kane, ya ce nasarar da kungiyarsa ta samu a kan Man U a Old Trafford sun isar da wani babban sako.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Sky Sports, dan wasan da ya ci kwallo daya a lokacin da Spurs ta lallasa Manchester United da ci 3-0.

Ya ce: "Mun isar da babban sako ne mu zo nan kuma mu yi nasara kamar yadda muka yi - babban sako ne. Mun so mu fara wannan kakar da kafar dama kuma mun samu nasarori uku cikin wasanni uku. Mun fara da sa'a."

Kane ya ce 'yan kungiyarsa ta Tottenham ba su yi wasa da kyau ba kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma kwallon da ya ci bayan an dawo daga hutun ta yi matukar taimaka wa kungiyar sosai.

Bayan Kane ya ci kwallon ne dai Lucas Maura ya zura kwallaye biyu a ragar Manchester United.

Wannan ya sa Tottenham ta zama ta biyu a teburin gasar Firimiya yayin da take da maki daya da Liverpool, wadda ke saman tebur, sai dai kulob din su Mohammed Salah ya fi ta yawan kwallaye.

No comments

Theme images by fpm. Powered by Blogger.