Subahanallah! Ambaliyar Ruwa Mai Martaba Sarkin Auyo yayi kuka a gaban jama’a
Subahanallah! Ambaliyar Ruwa Mai Martaba Sarkin Auyo yayi kuka a gaban jama’a
Mun ji labari cewa Mai Garin Kauyen Auyo Alhaji Umar Baffa ya fashe da kuka a gaban Jama’a bayan ya ga yadda ruwa ya jawo annobar da ci dinbin gidaje da dukiyoyi har ma da dabbobi a Garin na Auyo da ke cikin Jihar Jigawa.
Ambaliya ta ci Garin Auyo da ke cikin Jihar Jigawa
Mai Martaba Umar Baffa ya sheka kuka ne a fili bayan ya ga yadda ruwa ya shanye kusan kaf Garin na Auyo da sauran Kauyukan da ke gefe. Sarkin Auyon Hadejia Alhaji Baffa yace mutanen sa a kalla 3 ruwan ya kashe...
Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridun Kasar nan. Sarkin yace an yi asarar dukiya ta sama da Naira Biliyan 3.5 a dalilin wannan musiba da ta auku. Kogin Hadejiya zuwa Jama’are ne dai ya jawo wannan ambaliyar...
Sai da aka yi kusan kwana 2 ruwan dufana yana kwararowa daga Kogin zuwa Auyo inda ya shanye garin. Bayan nan kuma ruwan ya ci kauyukan da ke gefe irin su Jura, Rafeji, Uza, Gamakwai, Zabaro da kuma Ayama.
A dalilin asarar da aka yi na gidaje da gonaki da sauran dukiyoyi ne Sarkin ya fashe da kuka a Ranar Asabar dinnan. Wani ‘Dan kasuwa Alhaji Isa Auyo sai da yayi asarar manyan motoci fiye da 10 cike da takin zamani...
Yanzu dai mutanen Garin Auyo sun ruga zuwa Garuruwan da ke makwabtaka domin su samu matsuguni. Sarkin Garin ya nemi Gwamnatin Tarayya ta sa Jihar Jigawa cikin wadanda ke neman agaji na gaggawa a kasar...
Mai martaba Umar Baffa ya nuna takaicin sa na wannan abu da ya faru a kasar sa. Sarkin yace a 2001 an taba samun shigen irin wannan ambaliya, sai dai asarar ba za ta kamantu da abin da ya auku a wannan karo ba...
Sarkin dai ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kawo karshen wannan musiba na ambaliya inda ake tunani ruwan yana barkowa ne tun daga Kogin Kongo wanda ya keto zuwa Kamaru har ya kawo nan kusa zuwa Kasar Chad...
No comments