Kalli Photunan] Yadda fitattun jarumai suka raya ranar samun yancin Nijeriya
[Kalli Photunan] Yadda fitattun jarumai suka raya ranar samun yancin Nijeriya
Maryam Yahaya tayi adon taya Nijeriya murnar cika shekara 58 da samun yanci
Ranar litinin 1 ga watan Octoba al'ummar Nijeriya sun waye gari suna murnar zagayowar ranar samun yanci, suma jaruman arewa sun raya wannan ranar farin ciki.
Jaruman sun raya wannan ranar ta sakon da suka wallafa a shafukan su na kafafen sada zumunta.
Cikin su akwai mawaka da fitattun jaruman masana'antar kannywood.
Jarumai kama daga Sani Danja, Ali Nuhu, Maryam Yahaya, Hafsat Idris, Classiq, Nafisa Abdullahi, Rahama Sadau, Yakubu Muhammed zuwa Mansura Isa sun raya zagoyowar wannan rana.
Wasu da dama sun wallafa hotuna na musamman da suka dauka na taya murnar bikin cika shekara 58 sanye da riguna mai dauke da launin kasar tare da yin ado masu jan hankali.
Hakazalika wasun su sun kuma wallafa hotunan tutar Nijeriya a shafin su tare da rubuta sakon taya murna.
No comments